Hamas da Fatah sun kulla yarjejeniyar sulhu

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Fatah da Hamas sun fara rikici ne tuun lokacin da akayi zaben shekara ta 2006.

Bangarorin Palasdinawa na Hamas da kuma Fatah sun sanya hannu akan wata yarjejeniyar sulhu a birnin Alkahira.

Wannan dai wani kokari ne na dinke barakar da ta biyo bayan kin amincewar Fatah da nasarar da Hamas ta samu a zaben shekara ta 2006.

A zaman da suka yi a birnin Alkahira na Masar, shugabannin bangarorin na Palasdinawa sun cika burin yawancin larabawa ne da ke da fatan ganin an kawo karshen sabanin cikin gida da ke raunana kokarin 'yantar da Palasdinawa.

In aka tambayi akasarin Falasdinawa, za su ce suna maraba da wannan yarjejeniya; amma fa suna kuma kaffa-kaffa.

Ko da ya ke an sa hannu a kan takardar yarjejeniyar, ba lallai ne ta yi aiki a zahiri ba, domin bambance-bambancen da aka samu tsakanin Fatah da Hamas sun jawo mummunan rashin jituwa.

Wata mata wadda mijinta mai goyon bayan Hamas ya mutu bayan an lakada mishi duka a gidan yarin Fatah shekaru uku da suka wuce ta sahaidawa BBC cewa batun hadin kan Falasdinawa abu ne mai kyau amma ba za ta tabe yafewa Fatah ba.

Ta kuma ce tana fargabar duka yunkurin zai iya tashi a banza.

Sai dai duk da haka wannan ce kwakkwarar shaida ta farko cewa tunzurin da ya mamaye gabas ta Tsakiya bana zai sauya akalar rikicin da ke tsakanin Falasdinawa da Isra'ila wanda ya ki ci ya ki cinyewa.

Sabbin shugabannin kasar Masar ne dai suka shiga tsakani aka cimma wannan yarjejeniya tsakanin Hamas da Fatah.

A cewar wasu daga cikin wadanda suka shirya sasantawar, a baya tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak ne ya hana a sasanta kamar yadda Amurka da Isra'ila suka bukaci ya yi.

A yanzu dai shugabannin Isra'ila za su mai da hanakali ne wajen zakulo matakan da ya dace su dauka don tunkarar wannan sauyi da aka samu a tsakanin Falasdinawa da ma al'ummar yankin baki daya.

A tsakanin Hamas da Fatah kuwa, akwai sauran batutuwa da dama da ka iya sawa a gwara kai, ciki har da dangantaka da Isra'ila: shin za a hau teburin shawarwari da ita ne? Shin za a amince da wanzuwar ta ne ko kuma a'a?.