Zaa tuhumi jami'an Libya uku

Luis Moreno-Ocampo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luis Moreno-Ocampo

Babban mai gabatar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ya ce ya kudiri aniyyar samun wasu jami'an Libya su uku da aikata laiffukan keta hakkin bil'adama nan da wasu makonni masu zuwa.

Da ya ke jawabi a gaban kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, babban mai gabatar da karar Luis Moreno-Ocampo, ya ce a binciken da aka gudanar, an gano wasu shaidu dake nuna harbin masu zanga- zangar lumana, tare da azabtarwa da kuma hukunta wadanda ake zargin suna adawa da gwamnatin Libya.

Wakiliyar BBC ta ce Mr Ocampo ya ce zai bukaci sammacin kame mutane uku wadanda bincike ya nuna cewa suna da hannu dumu-dumu wajen aikata laiffukan keta hakkin bil'adama.