Ina aka kwana da kasafin kudin Nigeria?

Yayin da wa'adin majalisar wakilan Nigeria na Jamhuriyya ta hudu ke dab da karewa, rahotanni na nuna cewa kimanin kudirorin doka sama da dari uku ke gaban majalisar,.

Kudurorin da ke dakun amincewar majalisar dai sun hada da na kasafin kudin kasar na wannan shekarar.

Bisa doka dai wajibi ne majalisar ta zartar da kudurorin kafin cikar wa'adin nata ko kuma su shiririce.