An tsaurara tsaro a filayen jiragen saman Najeria

Filin jirgin saman Lagos
Image caption Filin jirgin saman Lagos

Hukumomin tsaro a Najeriya na kara tsaurara matakan tsaro a filayen jiragen sama na kasar.

Masu sharhi kan al'ammura dai na ganin cewa wannan mataki ba zai rasa nasaba da kashe shugaban kungiyar Al-Qaida, Osama Bin Ladin da dakarun Amirka suka yi ba.

Najeriya dai ta taba samun kanta cikin sahun kasashen da Amirka ta sawa ido a kan ta'addanci, tun bayan yunkurin da bai samu nasara ba da awni dan Niajeriya, Umar farouk Abdulmutallab ya yi na tarwatsa wani jirgin saman Fasinja dake kan hanyar sa ta zuwa Amirka.

Jirage da dama ne ke tashi kowace rana daga Najeriya domin zuwa Turai da kuma Amirka.