Kotu ta sallami Nuhu Arzika a Nijar

Tutar Jumhuriyar Nijar
Image caption Tutar Jumhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijar kotu ta sallami dan gwagwarmayar kare hakkin dan adam din nan Malam Nuhu Arzika har sai alkali mai bincike ya kammala bincikensa game da tuhumar da ake masa ta cin zarafin koyun tsarin mulki a shekara ta dubu 2 da 9.

Kotun ta saki Nuhu Arzikan ne a yau,bayan ya kwashe kwanaki 84 a gidan yari na birnin Yamai.

A ranar 10 ga watan fabrairun da ya gabata ne dai wata hukumar yan sanda ta kira Malam Nuhu Arzika tare da mika shi ga kotu; daga bisani kuma kotun ta tura shi gidan yari bisa zarge zarge da dama.

Daga ciki har da tuhumar da kotun ta yi masa cewa ya muzanta shari'a tare da kin mutunta matakin da kotun tsarin mulki ta yanke na hana tsohon shugaban kasa Tandja Mamadou yin zaben raba gardama domin zarcewa da mulki.