Amurka ba za ta nuna hotunan gawar Osama ba

Shugaba Obama Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama ya ce ba zasu fitar da hotunan gawar Osama bin Laden ba, saboda hakan zai iya yin barazana ga tsaron Amurka.

Tun lokacin da aka kashe shugaban kungiyar Al-Qaeda ne dai ake ta muhawara a Amurka game da fitar da hotunan Osaman, don bada tabbacin cewa an kashe shi.

Shugaba Obama ya ce gwajin da aka yi na kwayoyin halitta ya nuna cewa mutumin da aka kashe Osama Bin Ladan ne.

Sai dai wasu 'yan kasar sun bayyana matakin da Obama ya dauka da cewa, ba zai wadatar da mutane ba.

Tsohon magajin birnin New York, Rudy Giuliani ya ce, duk da kin amincewar Amurka na fitar da hotunan, hakan ba zai sanya mutane su gaza samunsu ba.

Ya kara da cewa fitar da hotunan ne zai kawar da shakkun da mutane ke yi kan kisan Osama Bin Ladan.