Pakistan ta zargi hukumomin leken asirin duniya

Hakkin mallakar hoto Google GeoEye
Image caption Taswirar garin da aka gano marigayi Osama sanan kuma aka kashe shi.

Pirayim Ministan Pakistan, Yusuf Raza Gilani ya zargi hukumomin leken asiri na duniya da daukar wani abu daga cikin zargin gazawar kasarsa na kasa gano Osama Bin Ladan.

Haka kuma yayi kiran samun taimako a yaki da ta'addanci da tsatstsauran ra'ayi, yana mai cewar Pakistan ba za ta iya yi ita kadai ba.

Pirayim Minista, Yusuf Gilani na magana ne a Paris, a inda ga alama zai fuskanci tsauraran tambayoyi daga shugabannin Faransa daga bisani game da gazawar hukumomin leken asiri na Pakistan.

Yusuf Raza Gilani, wanda ka iya fuskantar tambayoyi masu zafi daga hukumomin Faransa nan gaba a yau dangane da kasa gano maboyar Osama bin Laden da jami'an leken asirin Pakistan suka yi, ya ce kasarsa na bukatar taimako a yakin da take yi da ta'addanci da kuma tsattsauran ra'ayi.

Laifin gazawa

Da ya ke jawabi a Paris babban birnin kasar Faransa, Mista Gilani ya dora laifin gazarwar jami'an kasar tasa a kan hukumomin leken asiri na duniya.

Jiya Talata ne dai Ministan harkokin wajen, Faransa Alain Juppe, ya ce kasa gano cewa Osama na zaune a wani gida mai nisan kasa da kilomita daya daga wata cibiyar sojin Pakisatn ya daure masa kai.

Tun da farko dai kasar ta pakistan ta yi fatali da kalaman da ke cewa Pakistan ba ta boye sirri shi ya sa Amurka ba ta amince da ita ta tsegunta mata bayanan shirin kai hari gidan Osama ba.

Sakataren harkokin wajen Pakistan, Salman Bashir, ya shaidawa BBC cewa wadannan kalamai masu daga hankali ne.

A cewarsa, ba irin gudummawar da Pakistan ba ta ba Amurka da ma sauran kasashe ba a yunkurins u na kawar da ta'addanci:

"Jami'an hukumar leken asiri ta Pakistan, wato ISI, ne suka kama duk kusoshin kungiyar Alkaida wadanda aka kama a shekarun da suka gabata a birane da garuruwan Pakistan; ina kuma ganin ya kamata a tuna da wannan.

"Don haka, a gani na, maganar da ke tasowa lokaci zuwa lokaci cewa ba a yarda da mu ba ba ta dace ba." In ji Bashir

Mista Bashir ya kuma ce Pakistan ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa Amurka ta gano inda Osama bin Laden ya ke a garin Abbottabad.

"Gaskiyar magana ita ce jmi'an leken asiri na kasar mu ne suka nunawa jami'an leken asiri na Amurka wannan wuri tun da dadewa.

"Ba shakka jami'an na Amurka suna da kayan aiki na zamani don tantacewa da tabbatar da bayanai, Amma kuma Pakisatn ta taka rawa a wannan abin da ake kira nasarar da ka samu a yaki da ta'addanci a fadin duniya, shi ya sa kalamai irin wadannan ke daga mana hankali."

Wani mai magana da yawun ma'aikatar tsaro ta Afghanistan, Janar Zahir Azimi, ya ce yana fatan yanayin tsaro zai inganta a yankin bayan kisan Osama bin Laden.

Sai dai ya yi gargadin cewa mutuwar shugababn kungiyar Alqa'ida ba zai kawo karshen ayyukan ta nan ta ke ba.