Kungiyoyin Palasdinu za su sasanta da juna

Shugabannin Palasdinawa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kungiyoyin Palasdinu za su sasanta da juna

A yau Laraba ne bangarorin Palasdinawa na Hamas da kuma Fatah za su sanya hannu akan wata yarjejeniyar sulhu a birnin Alkahira.

Wannan dai wani kokari ne na dinke barakar da ta biyo bayan kin amincewar Fatah da nasarar da Hamas ta samu a zaben shekara ta 2006.

A zaman da za su yi a birnin Alkahira na Masar, shugabannin bangarorin na Palasdinawa za su cika burin yawancin larabawa ne da ke da fatan ganin an kawo karshen sabanin cikin gida da ke raunana kokarin 'yantar da Palasdinawa.

Da alama wannan sasantawa ba za ta yiwa Israela dadi ba.