Bude yakin neman zabe a Agadez

Jamiyyun siyasa a jamhuriyar Niger sun soma tsokaci a kan yadda za su tunkari zaben yan majalisar dokoki na kasa da za a yi ranar 15 ga wannan wata a jihar Agadez.

Hukumomin kasar dai sun ce a ranar Juma'amai zuwa 6 ga wata ne za'a bude yakin neman zabe na tsawon kwanaki 7 a fadin jihar.

Wasu yan majlisar dokoki 6 ne dai za 'a zaba a jihar domin cika gurubun, bayan rusa zaben farko da aka yi wanda kotun tsarin mulkin Niger ta yi a kan hujjar , wani dan takara ya ajiye takardun shaidar ilimi na bogi.

Sai dai a wannan karo, kotun tsarin mulki ta baiwa dukan jamiyyu da yan takara masu zaman kansu yancin shiga takarar .