ACN ta ce a kai kasuwa, kawance da PDP

A Najeriya, yayin da hankali ya koma kan rabe- raben mukamai bayan kammala zabe a kasar, jam`iyyar adawa ta ACN ta ce ba za ta shiga gwamnatin hadin-gwiwa da jam`iyyar PDP mai mulkin kasar ba.

Jam'iyyar ta ACN ta ce akwai bambancin akida tsakanin su da jam`iyyar PDP don haka hanyar jirgi daban, ta mota.

Jami'yyar ta ACN ta ce duk da dai Jam'iyyar PDP ba ta riga ta yi mata tayi ba, ta ce ta aikewa da PDP da sakon kada ta fara domin ba za ta amince ba.

Jami'yyar ta ACN ta kafa hujjar cewa an yi rashin gaskiya a zaben bana, ta hanyar amfani da kudaden al'umma ta hanyar da basu dace ba, wadda ita Jami'yyar ACN ke ganin amincewa da kulla kawancen gwamnatin hadin- gwuiwa da Jami'yyar PDP kamar mara mata baya ne akan abubuwan da ta yi da suka saba doka.