Babangida na son mulki ya dawo Arewa

Tsohon shugaba, Ibrahim Babangida
Bayanan hoto,

Babangida na son mulki ya dawo Arewa

Tsohon shugaban Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce idan har ana adalci ya kamata mulki ya koma Arewa a shekarar 2015.

Janar Babangida ya kara da cewa, babu wata yarjejeniya da suka kulla da shugaba Goodluck Jonathan gabanin zaben da ya gabata.

Ya ce bisa tsarin karba- karba na jami'yar PDP da aka soma amfani da shi tun shekarar 1999, dole ne mulki ya koma Arewa a 2015.

Janar din ya nuna gamsuwarsa da zabukan da aka yi, duk da yake ya ce, akwai kalubale da dama