Al Qaeda 'ta tabbatar da mutuwar bin Laden'

Osama bin Laden Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Osama bin Laden

Wata sanarwar da aka ce ta fito daga kungiyar al Qaeda, wadda ta tabbatar da mutuwar Osama bin Laden, a yanzu haka tana yawo a shafufukan intanet.

An wallafa sanawar ce a wasu shafufukan intanet masu yawa, na masu kishin Islama.

Sanarwar na cewa, za a dauki fansa, kuma murnar Amirka game da mutuwar Osama bin Laden, za ta koma ciki.

Haka kuma, sanarwar ta yi alkawarin cewa, za a watsa faifan muryar da aka nada ta Osama bin Laden mako guda kamin mutuwar sa.

Yau shugaban Amirka, Barack Obama, zai gana da wasu daga cikin zaratan sojojin kasar da suka kai farmaki a Pakistan, wanda yayi sanadiyar kashe jagoran kungiyar al-Qaedan, Osama Bin Laden, a ranar Lahadin da ta wuce.