An kashe mutane dayawa a Bauchi

Jahar Bauchi a taswirar Najeriya
Image caption Jahar Bauchi a taswirar Najeriya

A jahar Bauchi an kashe mutane kimanin 16 a karamar hukumar Bogoro, a sakamakon wani farmaki da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kai a daren jiya. An dade ana fuskantar tashe-tashen hankula na kabilanci da addnini a yankunan Bogoro da Tafawa Balewa na Bauchin.

Bayanai sun ce an kai harin ne a kauyen Kurum dake karamar hukumar Bogoron.

An kona gidaje kimanin 20, kana aka kashe wajejen mutane 16 daga cikin mazauna kauyen. Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Bauchi, Mista Anaman John Abbakassanga, ya ce a yanzu haka jami'an tsaro na sintiri a yankin da lamarin ya faru, kuma su na cigaba da neman wadanda su ka yi aika-aikar.