Amirka da Ghana zasu yaki fataucin miyagun kwayoyi

John Atta Mills, Shugaban Ghana
Image caption John Atta Mills, Shugaban Ghana

Kasashen Ghana da Amurka sun yi alkawarin taimaka ma juna, wajen yaki da masu safarar miyagun kwayoyi daga kudancin Amurka zuwa yankin yammacin Afrika.

Kasashen biyu sun bayyana wannan matsayi ne, bayan wata ganawar da aka yi a Ghana tsakanin sassan biyu.

Ambasada William Brownfield, karamin sakataren gwamnatin Amurkan mai kula da yaki da masu fataucin miyagun kwayoyi da kuma aiwatar da dokokin kasa da kasa, shine ya jagoranci tawagar Amurkan zuwa Ghana.

Bangarorin biyu sun cimma matsayar ne a birnin Accra a yau.

Mataimakin shugaban Ghana, Mr. John Mahama, shine ya wakilci gwamnatin Ghanar a wajen ganawar.