Takaddama a Kungiyar kwadago reshen Gombe

A Najeriya wata rigima ta kunno kai a cikin hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC, reshen Jihar Gombe, inda wasu daga cikin kungiyoyin ke kauracewa dukkan hidimomi na kungiyar a matakin Jiha.

Zabukan shugabannin kungiyar ne suka dada fito da rigimar fili, inda wasu ke zargin cewa an aikata ba daidai ba a zabukan domin kawo cikas ga kungiyar a jihar.

Baya ga haka kuma bikin ranar ma'aikata ta duniya da aka yi kwanan nan, kashi biyu aka yi a jihar ta Gombe.

To sai dai kuma shugabannin kungiyar kwadagon na cewa wadanda ke zargin an yi masu ba daidai ba, basu da wata hujja mai karfi.