A Najeriya, yau ake kammala zabe a Jihar Imo

A Najeriya, a yau ne ake sa ran gudanar da karashen zaben gwamna da na 'yan majalisar dokoki, a wasu kananan hukumomi hudu da wata unguwa a Jihar Imo.

Hukumar zaben Najeriya, INEC ta tura kwamishinonin zabe na tarayya guda hudu, da wasu kwamishinonin zabe na jihohi hudu, da kuma jami'an hukumar na wasu jihohi, domin su kula da gudanar zaben na yau.

Wannan kuma ya faru ne bayan da aka kakkabe hannun dukkan jami'an hukumar zaben jihar ta Imo, daga wannan zaben.

Ana ganin zaben na yau zai kasance raba gardama tsakanin Gwamnan Jihar dake kan mulki da kuma dan takarar Jam'iyyar PDP Chief Ikedi Ohakim da Oweli Rochas Okorocha dan takarar jam'yyar ta APGA.