Gwamnan jihar Imo ya sha kaye

A Najeriya, jam'iyyar adawa ta APGA ta sami nasarar lashe zaben kujerar gwamnan jihar Imo,wanda aka karasa a ranar Juma'a.

Dan takarar jam'iyyar ta APGA dai, Owelle Rochas Okorocha ya sami nasarar ce da gagarumin rinjaye a kan dan takarar jam'iyyar PDP da ke kan mulki, Cif Ikedi Ohakim.

Fafesa Hilary Edoga da ya bayyana sakamakon ya ce Mr Okoracha ya samu kuriu dubu dari uku da talatin da shidda da dari takwas da hamsin da tara yayinda da shi gwamnan jihar Imo, Ihedi Ohakim ya samu kuri'u dubu dari biyu da casain da dari hudu da casain da shidda.

An gudanar da zaben ne a jiya Juma'a a wasu kananan hukumomi hudu na Jihar ta Imo.

Sai dai sakamakon zaben be hada na ankin karamar hukumar Oguta ba, saboda soke zaben yankin da hukumar tayi a jiya biyo biyan wata takaddama wadda ta hana a karasa zaben a jiya.

Bayyana sakamakon zaben dai ya kawo karshen jiransa da kuma zaman dar-dar da ake ta yi a jihar ta Imo.