Taro kan rikicin kasar Libya

Shugaba Gaddafi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Za a yi taro kan kasar Libya

Kasashen duniyar da ke taka rawa a rikicin Libya za su yi taro a Italiya a yau Alhamis domin duba irin cigaban da aka samu a kokarinsu na tallafawa 'yan tawayen Libya da ke yakar Kanar Gaddafi.

Kusan watanni uku bayan soma shi, yakin na Libya yana neman ya shiga halin kwan-gaba kwan- baya.

Masu halartar taron dai sun hada ne da kasashen kungiyar tsaro ta NATO, da kuma wasu kasashen larabawa.

Majalisar dinkin duniya dai, na gudanar da bincike kan take hakkin bil adama da ake yi a kasar Libya, sakamakon rikicin da ke faruwa.