An rusa kwamitin gudarnawar majalisar dokokin Nijar

Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou
Image caption Shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar, kotun tsarin mulkin kasar ta rusa kwamitin gudanarwa na majalisar dokoki, bayan ta same shi da laifin keta kundin tsarin mulkin kasar.

Wannan ya biyo bayan wata kara ce da 'yan majalisar dokokin, bangaren kawancen adawa na ARN suka shigar a kwanan baya, suna kalubalantar matakin da bangaren masu rinjaye na majalisar ya dauka, na hana masu wani adadi na mukamai a kwamitin.

A lokacin dai 'yan adawar sun kaurace wa majalisar zuwa wani dan lokaci, domin neman hakkokinsu.

Kotun tsarin mulkin ta ce, ya kamata a ba kawancen na ARN mukamai 3 daga cikin 13 a kwamitin gudanarwar majalisar dokokin, a maimakon biyun da aka basu tun farko.