Gwamnati Amurka ta saki wasu bidiyon Osama

Image caption Shugaba Obama na Amurka

Ma'aikatar tsaron Amurka ta saki wasu faya fayan bidiyon Osama Bin Laden wadanda aka kwaso lokacin da aka kai farmaki gidansa a ranar lahadi din da ta gabata.

Daya daga cikin faya fayan ya nuna Osama lokacin da yake hada wani sako wanda bai kai ga saki ba, yayin da wani kuma ya ke nuna shugaban na Al Qa'ida yana kallon wani shirin talabijin da ake gabatarwa a kansa.

Wani baban jami'in leken asiri Amurka ya ce harin da aka kai, da yayi sanadiyar mutuwar Osama Bin Laden a Pakistan ya samar da bayanai siri mafi girma da aka taba samu, daga wurin wani da ake zargin shi dan ta'ada ne.

Ya ce a bayane take cewa gidan da aka kashe Osama Bin Laden shi ne cibiyar da kungiyar Al Qaeda ke bada umurni.