Bincike kan lamarin bin Laden a Pakistan

Osama bin Laden Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Osama bin Laden

Manyan jami'an tsaro a Pakistan sun bada umurnin a gudanar da bincike a kan abinda suka kira: gazawar hukumomin leken asirin kasar, wajen gano maboyar Osama bin Laden a Pakistan din.

A lokacin wata hira da manema labarai, shugabannin sojan Pakistan sun koka kan yadda Amirka ba ta sanar da su ba, kamin ta kai hari a gidan jagoran kungiyar al Qaeda, Osama bin Laden, a ranar Lahadi da dare, inda ta hallaka shi.

Sojan na Pakistan suka ce, a halin yanzu suna tsare da ukku daga cikin matan Osama bin Laden.

Suka ce daya daga cikin matan, 'yar kasar Yemen, ta shaidawa masu yi mata tambayoyi cewa, ita da mijin nata, marigayi Osama bin Laden, sun kwashe shekaru biyar suna zaune a wani daki, a cikin gidan da aka kashe shi.

An kuma gano kananan yara 13 a cikin gidan.