Me jama'a ke jira daga sabuwar gwamnatin Najeriya?

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Yau shekaru goma sha biyu kenan da ake gudanar da mulkin demokradiyya ba kakkautawa a Najeriya.

Bayan da ta shirya zabe a shekarar 1999, gwamnatin mulkin soja ta wancan lokaci, karkashin jagorancin Janar Abdusslami Abubakar, ta mika mulki ga gwamnatin farar hula ta jam'iyyar PDP, karkashin jagorancin shugaba Olusegun Obasanjo, wanda aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar ta 1999.

Tun daga wancan lokaci ne kuma aka mayar da wannan rana ta zama ranar Demokradiyya a Najeriya.

Tun daga 1999 din har ya zuwa yanzu, jam'iyyar ta PDP ce ke mulkin kasar.

Sai dai masu sharhi kan al'amurran yau da kullum na cewa, duk da irin nasarorin da gwamnatin PDPn ta ce ta samu a wasu fannoni a tsawon wannan lokaci, akwai fannoni da dama da gwamnatin ta gaza.

To yayinda a jibi za'a rantsar da shugaba Goodluck Jonathan tare da gwamnonin wasu jihohin Najeriyar, batun da yanzu haka ke jan hankalin 'yan Najeriyar da dama, shi ne na irin kalubalen dake jiran sababbin hukumomin.

A kan haka ne shirin Ra'ayi Riga na yau ya maida hankali.