'Yancin aikin jarida a kasashen Afurka.

Muhawara kan aikin jarida
Image caption Muhawara kan aikin jarida

A wannan makon ne aka gudanar da bikin ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya.

Shin ko a kasashe masu tasowa 'yan jarida na da 'yancin gudanar da ayyukansu kamar yadda ya kamata, wace rawa ya kamata su taka wajen karfafa tsarin dimokradiyya?

Majalisar Dinkin Duniya ta kebe Ranar 3 ga watan Mayun kowace shekara domin bikin ranar 'yancin 'yan jarida ta duniya.

Ana amfani da wannan rana ce domin wayar da kan jama'a game da muhimmancin 'yancin 'yan jarida, a kuma tunatar da gwamnatoci kan hakkin da ya rataya a wuyansu na mutunta 'yancin fadin albarkacin baki, kamar yadda yake a karkashin dokar kare hakkin dan adam ta majalisar dinkin duniya.

Taken bikin na bana dai shi ne muhimmancin 'yancin 'yan jarida ga tsarin demokradiyya.

Jama'a da dama sun yi amannar 'yan jarida na taka rawa wajen bankado irin ta'asa da cin hanci da rashawar da ake zargin wasu shugabanni na aikatawa, tare da kawo sauyi a kasashen da gwamnatocinsu ba sa bin tsarin demokradiyya.

Alal misali, 'yan jarida sun taka muhimmiyar rawa a juyin juya halin da ake samu yanzu haka a yankin gabas ta tsakiya, da ma wasu kasashen arewacin Afirka.

Cikin bakin da aka gayyato a shirin Ra'ayi Riga domin tattaunawa kan batun shun hada da, Ministan sadarwa na Nijar, Alhaji Salifou Labo Boushe, da Alhaji Shu'aibu Usman Leman, babban sakataren kungiyar 'yan jarida ta Nijeriya, da kuma Alhaji Awwalu Salihu, na hukumar kula da kafaafen yada labarai ta Nijeriya, NBC.