A yau za'a zubawa wani gubar acid a idanunsa

Image caption Wasu mata a kasar Iran

A Iran nan gaba a yau ne za'a zubawa wani mutum gubar Acid a idanunsa a matsayin wani hukuncin watsawa wata mata gubar acid a fuska da mutumin ya aikata shekaru bakwai da suka gabata saboda ta ki amincewa ta aure shi.

Likitoci dai zasu fidda mutumin mai suna, Majid Mowahedi daga hayyacinsa kafin su zuba masa gubar ta Acid a idananunsa.

Movahedi ya kusanci Ameneh Bahrami a lokacin da take dawowa daga wurin aiki da yammacin wata rana a shekerar 2004.

Ta ce ta ga lokacin daya rike da wani gwangwani 'ja kuma ya watsa mata abin dake ciki a fuskarta.

Ameneh Bahrami dai ta samu munanan raunuka sakamakon konewa daga gubar acid, bugu da kari an yi mata aiki tayita fiye da ashirin domin a dawo mata da ganinta kuma a gyra mata fatar fuskar ta da ta lalace.

Sai duk da kulawar da ta rika samu a kasar Spain, Ameneh ta makance ta kuma ce ta ji dadin cewa mutumin da ya kai mata wanan hari shi ma zai ji abin da take ji

Majid Movahedi ya amince da hari a gaban wata kotu shekaru ukku da suka gabata.

Mahaifinsa ya yi kira ga Ameneh Bahrami akan ta tausaya masa.

Sai dai Ameneh ta tabatar da cewa tana son a aiwatar da hukucin kuma ta amince ta zuba masa gubar acid din da kanta