Bankin Duniya ya ba Nijar tallafin kudi

Image caption Alhaji Issoufou Mahamadou

Bankin duniya ya tallafawa jamhuriyar Niger da kudi kimanin dalar Amurka miliyan 120, kwatankwacin biliyan 55 na CFA.

Gwamnatin ta Niger dai za tayi amfani da wadannan kudaden ne wajen samar da ruwan sha, da yaki da cutta mai karya garkuwar jiki.

Ministan tsare-tsare na Niger din, Dr Amadu Bubakar Sise ne ya bayyana haka a jiya ta kafar yada labaran gwamnatin kasar.

Ya kuma ce daga cikin kudaden, gwamnatin kasar zata saka kimanin miliyan 45 a fanin ruwan sha,yayinda sauran kudaden kimanin miliyan goma na CFA za'a sakasu a fanin yaki da cuttar dake karya garkuwar jiki wato AIDS ko CIDA.

Shekaran jiya ne dai Niger din da bankin duniyan suka kulla yarjejeniyar bada wannan tallafi a wani mataki na maido da huldar da ke akwai tsakanin bankin duniyar da Niger, huldar da ta yanke sakamakon juyin mulkin da aka yi a kasar bara.