Shin PDP ta fara rabon mukamai a Najeriya?

Bayan kammala zabe a Najeriya da ya janyo cece- kuce da asarar rayuka da dukiya, rahotanni daga Kasar na cewa hankalin Jam`iyyar PDP mai mulki ya koma kan yadda za ta raba mukamai tsakanin `ya`yanta da kuma abokan tafiyar ta da ke shiyyoyi daban-daban na kasar.

A cewar rahotannin an samu kiki- kaka tsakanin Shugaban Kasar Dr Goodluck Jonathan da kuma wasu jiga- jigan Jam`iyyar PDP, dangane da tsarin karba-karba da Jam`iyyar ke tunanin bi wajen rabon mukaman.

Sai dai a nata bangaren, Jam`iyyar PDP ta musanta haka, in da ta ce kawo yanzu bata kaiga matakin rabon mukaman ba.

A bangare guda kuma Jam'iyyar adawa ta CPC ce ta shigar da `kara a gaban kotun sauraren `kararrakin zaben shugaban kasa, inda take `kalubalantar zaben shugaba Goodluck Jonathan na jam'iyar PDP, a matsayin wanda hukumar zaben `kasar ta ce shine ya lashe zaben da aka gudanar a watan jiya.

Jam'iyyar ta shigar da karar da yammacin jiya lahadi, gabanin cikar wa'adin da aka kebe na shigar da `kara akan zaben Shugaban Kasar, dake cika a yau litinin.

A cewar Jam'iyyar ta CPC, wasu daga cikin hujjojinta na shigar da karar sun hada da zargin tafka magudi, da kuma rashin bin dokokin zabe, inda ta ce zata gabatar da shaidu 151 don tabbatar da karar data shigar.