Nijar na bikin ranar yaki da zazzabin cizon sauro

A Jamhuriyar Nijar yau ne Hukumomin kiwon lafiyar Kasar ke bikin ranar yaki da zazzabin cizon sauro ta duniya a garin Kiota da ke cikin Jahar Doso.

Majalisar dinkin duniya ta kebe wannan ranar ne domin gwamnatocin kasashen duniya da kungiyoyi masu zaman kansu su kara yin nazari a kan illolin cutar tare da duba matakan da suka dace domin riga kafi.

A ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata ne dai ya kamata Nijar ta bi sahun kasashen duniya domin wannan biki, amma hakan bai samu ba saboda wasu dalilai.

A Kasar ta Nijar a shekarar 2010 alkaluman Hukumar yaki da zazzabin cizon sauron ya kiyasta mutane sama da Miliyan 3 da suka kamu da cutar ta zazzabin cizon sauro, daga cikinsu kimanin mutane dubu 4 sun rasa rayukansu, kuma galibi mata masu juna biyu da kananan yara 'yan kasa da shekaru 5 da haihuwa ne.