Dakarun Syria na ci gaba da kai samame

Dakarun tsaron Syria sun kara dannawa cikin yankunan kasar, a kokarin da suke na murkushe masu adawa da gwamnati.

Wakilin BBC ya bayyana cewa, bayan sallar Juma'ar da ta wuce, an kashe masu zanga zanga kimanin goma sha biyar a birnin na Homs.

Sojoji tare da tankunan yaki sun shiga wasu unguwannin birnin Homs na tsakiyar kasar, kuma wasu rahotanni na cewa an ji karar harbe-harbe, kuma an yi kame-kamen jama'a.

Gidan talabijin din Syriar ya ce, an kashe abinda ya kira: wasu masu dauke da makamai, wadanda ke yi wa gwamnati zagon kasa, kuma an kwato makamai da albarusai.

Haka ma, sojojin sun cigaba da kai farmaki a garin Banias na gabar teku, da kuma a kauyukan da ke kewayen birnin Der'a na kudancin kasar, mai fama da tashin hankali.