Dakarun Syria sun killace wani yanki na Damascus

Dakarun Syria sun killace wani yanki na Damascus Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani jami'in sojin Syria na sunturi a birnin Damascus

Rahotanni sun ce cikin dare tankunan yaki da jami'an tsaro sun killace wata unguwa da ke yammacin birnin Damscus na Syria, inda aka jiyo karar harbe-harbe da kuma fashewar abubuwa.

An kuma ce bakin hayaki ya yiwa unguwar, wadda aka yankewa wutar lantarki da wayar tarho, lema.

Rahotanni sun ce tun ranar Asabar da dare jami'an tsaro ke bi gida-gida, inda aka kama mutane da dama ciki har da mata.

Wani mai fafutukar kare hakkin bil Adama wanda ba a ambaci sunansa ba saboda a ba shi kariya ya shaidawa BBC irin bayanan da ya ke samu:

Ya ce wani mutum ya dauko mahaifiyarsa a kan babur zai kai ta asibiti, sai sojojin suka harbe shi; bayan harsashin ya shiga jikinsa sai ya fice ya shige jikin mahaifiyar.

Yunkurin ba-sani-ba-sabo

"Duk su biyun sun mutu. Yanzu haka kuma muna da mutane da dama--tsakanin dubu goma zuwa dubu goma sha-biyar--a gidan kaso. Yanayin ya yi muni matuka".

Wannan dai shi ne yunkuri na ba-sani-ba-sabo na baya-bayan nan da gwamnatin Syria ta fara don murkushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnatin.

Sojoji da tankunan yaki sun mamaye wani bangare na tsakiyar birnin Homs, wato birni na uku mafi girma a kasar, inda aka ba da rahotannin harbe-harbe, da kame-kame.

An kuma ba da rahoton mutuwar mutane da dama, ciki har da wani yaro dan shekaru goma sha-biyu.

Hukumomin kasar ta Syria dai sun ce an kashe sojoji da 'yan sanda shida a wannan yunkuri na baya-bayan nan da ta ce na kawar da 'yan ta'adda ne masu dauke da makamai.