An zargi jami'an Bangladesh da cin zarafin jama'a

bangladesh Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jami'an rundunar sun yi kaurin suna a Bangladesh

Babbar kungiyar kare hakkin bil adama ta duniya ta zargi rundunar kar-ta-kwana da gwamnatin kasar Bangladesh ta kafa da cin zarafin jama'a.

Rahoton na baya-bayan nan na kungiyar Human Rights Watch ya ce akalla mutane dari biyu ne ake zargin rundunar ta kar-ta-kwana da kashe mutane tun bayan da jam'iyyar Awami League ta karbi ragamar gwamnati a farkon shekarar 2009.

A cewar rahoton, duk da alkawuran da gwamnatin ta sha yi, babu wani jami'in rundunar da aka taba hukuntawa a kan kashe-kashen da kuma wasu laifukan keta hakkin bil Adama.

Gwamnatin dai ta ce rundunar 'yansandan tana fada ne kawai da bata-gari, kuma ana samu mace-mace ne yayin fito-na-fito tsakanin jami'an tsaro da masu aikata miyagun lafuffuka.

A yi wa rundunar kwaskwarima....

Sai dai wani mutum mai suna Manzurul Alam, wanda aka kashe dan uwansa yayin wani karon batta da rundunar a shekarar 2009 ya ce dan uwansa bai aikata wani laifi ba.

"Ba wani caji ofis din da ya ce dan uwan nawa bata-gari ne; jami'an rundunar ta kar-ta-kwana ne kawai suka ce shi bata-gari ne. Har yanzu kuma sun kasa kawo hujjarsu ta fadin hakan. Har yanzu dai muna jira mu ga an yi adalci; amma yanzu ba mu da sauran fata".

A titunan Bangladesh dai dakarun rundunar ta kar-ta-kwana masu sanye da bakaken tufafi da kyalle a daure a kansu tamkar jamfa ce a Jos.

A 'yan shekarun da suka gabata sun yi kaurin suna wajen rage aikata manyan laifuka da kuma hana masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama sakat, al'amarin da ya sa ake tsoronsu.

Kungiyar Human Rights Watch ta ce ya kamata gwamnatin ta yi wa rundunar kwaskwarima ta kuma hukunta jami'an rundunar wadanda aka samu da laifin kashe-kashe ba bisa ka'ida ba, ko kuma ta soke rundunar.