Majalisar dinkin duniya na son a dakatar da rikicin Libya

Shugabar kwamatin agaji na majalisar dinkin duniya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Majalisar dinkin duniya na son a dakatar da rikicin Libya

Shugabar hukumar jinkai ta majalisar dinkin duniya Valerie Amos, ta yi kira da a tsagaita wuta a Libya, domin ba da damar kai dauki ga masu bukata.

Shugabar hukumar ta bayyana kawanyar da aka yiwa tashar jiragen ruwan Misrata da cewa lamarin ya kazance.

A lokacin da take magana a kwamitin sulhu na majalisar, Madam Amos ta ce mutane da dama sun jikkata sakamakon rikicin Libyar.

Ta ce: ''Muna bukatar samun damar tabbatar da cewa wadanda suka jikkata kuma suke bukatar kulawar lafiya, sun samu hakan.Muna son mu tabbatar da cewa an shigar da kayayyakin kula da lafiya a yankunan kasar''.