Tarayyar Turai za ta bude Ofis a Benghazi

Catherine Ashton Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Catherine Ashton

Kungiyar tarayyar Turai ta ce tana shirin bude ofishinta a birnin Benghazi, na kasar Libya, yankin dake hannun 'yan tawaye.

Babbar jami'ar dake kula da harkokin kasashen waje ta kungiyar tarayyar turai, Catherine Ashton ta shaidawa majalisar tarayyar turan cewa matakin zai taimakawa gwamnatin 'yan tawayen.

Ta ce ta yi niyyar bude ofishi a Benghazi ta yadda kungiyar zata ci gaba da tallafin da ta amince ta ba 'yan tawayen, a kuma taimakawa fararen hula da gwamnatin rikon kwarya.

Mrs Ashton ta ce wannan zai hada da samar da tsaro da ababen more rayuwa ga jama'a.

Faransa da Italiya ne kadai suka amince da gwamnatin rikon kwaryar a cikin tarayyar turai baki daya.