Ana tumhumar tsegunta hannun jari a Amurka

Raj Rajaratnam Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Zai iya samun hukuncin shekaru ashirin a jarun

Wata kotu a New York tana tuhumar wani fitaccen mai harkar hada-hadar hannayen jari, Raj Rajaratnam, da laifin ba tsegunta sirrin hannun jarin wani kamfani.

Nufin hakan shi ne samun ribar jarin kafin sauran jama’a, abinda bai kan ka’ida.

Wannan ita ce shari'a mafi girma da ta shafi harkar hada hadar kudi.

Masu shigar da kara sun ce manajojin kamfanin Mr Raj-ratnam----- sun yi amfani da bayanan sirrin da suka samu ba bisa ka'ida ba domin samun ribar sama da dala miliyan sittin.

Masu shigar da karar dai sun dogara da shaidar da suka samu ta wayoyin da manajojin suka yi ta buga wa manyan jami'an kasuwar hannayen jari ta Wall Street a New York a lokacin.

Mr Rajratnam dai na iya fuskantar daurin shekaru 20.

Sai dai kuma lauyansa ya ce za su daukaka kara.

Mr John Dowd ya ce zamu daukaka kara kan wannan shari'a, mun fara da laifuka talatin da bakwai yanzu mun dawo goma sha hudu, haka za mu ci gaba.