'Yan tawayen Libya sun kama filin jirgin saman Misrata

'Yan tawayen Libya a Misrata Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption 'Yan tawayen Libya a Misrata

Dakarun da ke gaba da gwamnatin Libya sun ce sun kama filin jirgin saman Misrata, birnin da dakarun gwamnati suka yi wa kawanya.

Sun kama filin jirgin ne bayan kwashe kwana da kwanaki ana kazamin fada tsakanin 'yan tawayen da dakarun gwamnatin Gaddafi.

Wakilin BBC a birnin Benghazi ya ce ya sami labarin jama'a suna murna a kan tituna a birnin na Misrata, inda 'yan tawayen suka kuma kakkama tankokin da dakarun gwamnati da ke ja da baya suka gudu suka bari.

Misrata shi ne birni na ukku a girma a Libyar, kuma manazarta na cewa kama filin jirgin saman wani muhimmin ci gaba ne ga 'yan tawayen.