Sufeto Janar ya ce an yi zabe na adalci a Najeriya

'Yan sanda a Najeriya
Image caption Wace irin rawa suka taka

A Najeriya Rundunar 'yan sandan kasar ta gudanar da wani taro na manyan jami'anta domin yin nazari kan irin rawar da jami'anta suka taka wajen zabukan kasar da aka yi cikin watan da ya gabata.

Sai dai duk da cewa zaben ya gudana ba tare da wani tashin hankali mai yawa ba, an samu mummunan hargitsi bayan zaben a wasu sassan kasar, abinda kuma ya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi da dama.

Sai dai Alhaji Hafiz Ringim, Sufeto Janar na ‘yansandan Najeriyar, ya ce an yi zaben cikin ‘yanci da adalci.

Ya kuma ce ‘yan sanda sun taka rawarsu irin yadda ya kamata.

Y ace wanda kuma ke zargin ‘yan sandan da yin wani abu ba daidai ba, to ya je kotu.