'Ya kamata a bayar da diyya ga wadanda rikicin Najeriya ya shafa'

Wasu daga cikin mutanen da rikcin bayan zaben Najeriya ya shafa

A Najeriya, kungiyar kare hakkin bil Adama ta Civil Rights Congress ta ce ya kamata shugaban kasar ya biya diyya ga duk mutanen da rikicin da ya auku bayan zaben shugaban kasar ya shafa.

Kungiyar ta yi kakkausar suka ga furucin da gwamnati ta yi na baiwa iyalan matasan da ke yiwa kasa hidima wato NYSC diyyar naira miliyan biyar- biyar.

Shugaban kungiyar, Shehu Sani ya zargi gwamnati da nuna wariya da gazawa wajen tausayawa sauran jama'ar da suka rasa 'yan uwansu a lokacin rikicin.

Sai dai gwamnati ta ce ba zata baiwa sauran mutanen da rikicin ya shafa diyya ba, saboda har yanzu bata san adadinsu ba.

Masu yiwa kasar hidima goma ne dai rahotanni suka ce an kashe, biyo bayan zaben shugaban kasar na watan Afrilu.

Sai dai daruruwan mutane ne, baya ga masu yiwa kasar hidima suka mutu biyo bayan zaben shugaban kasar.