Kotun kolin Niger ta wanke wasu sojoji

Kotun kolin Niger ta ce ba ta gano wani laifi ba dangane da zargin da tsohuwar gwamnatin Janar Salou Djibo ta yi wa hafsoshin sojan nan guda 4 yunkurin juyin mulki da kuma kokarin kashe tsohon shugaban mulkin sojin.

Alkalin gwamnatin mai shigar da kara gaban kotun kolin ta Yamai ta fada wa kotun cewa binciken da aka yi bai tabbatar da wata kwakkwarar hujja da ke nuna sojojin sun so yin juyin mulki ba.

Sojojin , da a yyanzu haka suke gidan kaso sun hada da Kanar Abdullahi Bage ,da Kanar Amadu Diallo ,da laftana Kanar Abdu Sidiku Isa ,da kuma laftana Kanar Abubakar Amadu SANDA.

Yanzu haka kotun kolin ta Yamai ta ce ranar 19 ga wannan watan ne za ta yanke hukunci dangane da wannan shara'a.