Sabuwar zanga-zanga a Syria

Masu zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An gudanar da sabuwar zanga-zanga a Syria

Dubban dalibai ne suka gudanar da zanga-zanga a Aleppo, birni na biyu mafi girma a kasar Syria.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun tsaro sun yi amfani da kulakai wajen tarwatsa masu zanga-zangar.

A cikin dare ne dai dalibai suka gudanar da zanga-zangar, wacce suka fara daga harabobin dakunan kwanansu.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce daliban na neman a kawo karshen kawanyar da aka yiwa sauran biranen kasar ne, wadanda suka hada da Homs, Deraa, da Banias.

Biranen dai sune wuraren da masu zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Bashar al Assad suka fi karfi.