Gwamnatin Lagos ta hana bara

A Nijeriya, gwamnatin jihar Lagos, dake kudu maso yammacin kasar, ta kafa dokar hana bara, da kuma baiwa mabarata sadaka a kan tituna.

Gwamnatin ta ce duk wani da aka kama yana bai wa mabarata sadaka a kan titunan jihar zai iya fuskantar daurin shekara biyu a gidan kaso.

Matakin da gwamnatin jihar Lagos ta dauka , na daga cikin wadanda take dauka a cewarta, na tsabtace birnin Ikko daga matsalar mabarata, tare da mayar da birnin Ikko daya daga cikin birane mafiya tsabta a duniya.

Su dai mabaratan sun koka kan matakin, suna cewa zai raba su da hanyar samun abincinsu.

A baya, an sha kwasar mabaratan daga Lagos, ana mayar da su arewacin Nijeriya, amma makonni kadan bayan haka su sake komawa.