An kai karar Buhari kotun duniya

Janar Muhammadu Buhari
Image caption An kai karar Buhari kotun duniya

A Najeriya, wata kungiya da ke ikirarin tabbatar da dimokaradiyya da adalci ta ce ta kai karar Janar Muhammadu Buhari a gaban kotun duniya akan zargin furta kalaman tunzura jama'a a lokacin zaben kasar.

Kungiyar, maisuna Northern Coalition for Democracy and Justice, ta ce janar Buhari ne ya yi sanadiyar tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan jiya.

Jami'in kungiyar Yunana Shibkau, ya ce sun nemi kotun duniyar ta dauki mataki akan Janar Muhammadu Buhari da kuma sakataren jam'iyar CPC, Buba Galadima.

Sai dai a martanin da ya yi, Buba Galadiman ya ce gwamnatin kasar ce ta dauki nauyin 'yan kungiyar da zummar ganin ta ci zarafin Janar Buhari.

Ya ce a shirye suke su tunkari kotun duniya kan batun.