Mutane tamanin sun mutu a Pakistan

Wata mace data jikkata a harin da aka kai Pakistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taliban ta dauki nauyin kai hari a Pakistan

'Yan sanda a Pakistan sun ce fashewar wasu abubuwa guda biyu, ta yi sanadiyar rasuwar mutane kimanin tamanin tare da jikkata wasu da dama.

'Yan sandan sun ce fashewar ta auku ne a wata cibiyar horar da sojoji da ke arewa maso gabashin kasar.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce, yawancin wadanda suka rasu, kuratan soji ne wadanda ke shiga motocin da za su tafi da su, a lokacin da abubuwan suka fashe.

Kungiyar taliban dai ta dauki alhakin kai harin, inda ta ce ta kai shi ne domin ramuwar gayya bayan kisan da Amurka ta yi wa Osama Bin Laden.