Shugaban hukumar leken asirin Pakistan ya yi tayin yin murabis

Janar Ahmed Shuja Pasha
Image caption Janar Ahmed Shuja Pasha

Shugaban hukumar leken asirin Pakistan Janar Ahmed Shuja Pasha ya yi tayin ya sauka daga kan mukaminsa.

Hakan dai ya biyo bayan wasu tsauraran tambayoyi ne da ya fuskanta daga majalisar dokokin kasar, dangane da yadda dakarun kundumbalar Amurka suka kaddamar da harin da ya yi sanadiyyar mutuwar Osama Bn Laden.

Janar Pasha ya ce sai dai ba'a amince da tayin nasa ba.

An ambato shi yana cewar tambayoyin da 'yan majalisar suka yi ma sa masu tsauri ne, har ya ji cewar shine abokin gabar.

Tun da farko dai mayakan Taliban dake Pakistan sun ce suke da alhakin harin da aka kai cibiyar horar da sojoji a yau juma'a, harin da ya yi sanadiyyar mutuwar akalla mutane tamanin.

Wani mai magana da yawun 'Yan Taliban din, Ahsanullah Ahsan, ya ce hari ne na ramuwar gayya akan kisan Osama bin Laden.