NATO ta sake kai hari a Libya

Barnar da harin NATO ya haddasa
Image caption Barnar da harin NATO ya haddasa

Dakarun kawancen tsaron NATO sun kai karin farmaki a kan Turabulus, babban birnin kasar Libya.

An ji karar fashewar wasu abubuwa har sau uku a cikin dare, kusa da wani barikin soja da shugaban kasar Muammar Gadafi kan yi amfani da shi. Gidan Talabijin na Libya ya watsa wata murya da ake cewar ta Kanar Gaddafi ce, inda a cikin sakonsa yake zolayar dakarun kawancen.

Ya ce ba za su taba iya kama shi, ko halaka shi ba, domin yana cikin zuciyar al'ummar Libya.

Wani wakilin BBC a birnin na Turabulus ya ce muryar ba ta fito sosai ba, domin haka, zai yi wuya a iya tabbatar da cewa babu tantama muryar ta Kanar Gaddafi ce.