Syria za ta janye sojojinta daga birane biyu

Tankokin yakin Syria
Image caption Tankokin yakin Syria

Syria ta ce za ta janye sojoji tare da tankokin yakinta daga birnin Baniyas da kuma yankin birnin Deraa na kudancin kasar, bayan farmakin da sojojin suka kai don maido da doka da oda a yankunan.

Hakazalika gwamnatin Syriar ta ce za ta kaddamar da wani babban taron 'yan kasar cikin 'yan kwanaki masu zuwa, wanda zai duba batun sauye-sauyen da za a kawo a kasar.

Sai dai wasu majiyoyin 'yan adawa sun ce an yi jerin kame a yau, kuma sabon fada ya barke a kusa da birnin Homs, wanda hakan ya tilasta ma mutane da dama tserewa zuwa cikin kasar Lebanon.

Saboda haka 'yan adawan sun nuna shakku game da anniyar gwamnatin kasar ta sassantawa.