Isra'ila ta kashe Palesdinawa goma sha biyu

Palesdinawa na taimakawa wani da ya ji rauni Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Palesdinawa na taimakawa wani da ya ji rauni

Dakarun Isra'ila sun bude wuta a kan wasu masu zanga zanga a kan iyakokin kasar da Lebanon da kuma Syria. Rundunar sojan Lebanon ta ce an kashe mutane goma, an kuma raunata wasu sama da dari da ashirin.

Can kuma a kan iyaka da Syria, an kashe mutane biyu, an kuma raunata wasu kimanin ashirin, lokacin da masu zanga zangar, suka tsallaka wani shinge, suka shiga cikin yankin Tuddan Golan da Isra'ila ke mamaye da shi.

Duban Palasdinawa ne da magoya bayansu suka yi tattaki zuwa kan iyakokin, domin juyayin cika shekaru sittin da uku da kirkiro kasar Isra'ila.