Muna jiran hukuncin kotu a'kan Libya- Ocampo

Image caption Loius Moreno Ocampo

Kotun sauraren manyan laifuka ta duniya a birnin Hague na shirin yanke shawara a'kan ko ta amince da umurnin kama manyan jami'an gwamnatin Libya su uku bisa zargin aikata laifufkan yaki.

Yanzu dai babban me shigar da kara na kotun Louis Moreno Ocampo na bukatar alkalan su amince da samaci kamen, da ake ganin ya yadda da shi kansa shugaban libya kanar Gaddafi da shugaban leken asirinsa Abdullah Sanussi da kuma dansa Saif AL Islam.

Sai dai gwamnatin Libya ta ce ba zata saurari kotun ba, saboda kasashe kamar su Amurka basu sa hanu kan yarjejeniyar da kaiga kafuwar kotun ba.

Sai dai wasu gwamnatocin turai na ganin shellar samacin kamen zata sa sauran manyan jami'an gwamnatin Libya tserewa daga kasar bisa fargabar sune wadanda za'a kama nan gaba.