Sabbin shugabanin Majalisar dokoki Najeriya

A Najeriya 'yan majalisar wakilan kasar na cigaba da fafutikar lalubo sabbin shugabannin majalisar, duk kuwa da matsayin jam'iyyar PDP mai rinjaye a majalisar dake cewa, bangaren kudu-maso-yammacin kasar ne ya kamata ya riki wannan mukami.

Bakin wasu mambobin majalisar dai, kama daga 'yan jam'iyyar PDPn, zuwa 'yan jam'iyyun adawa ya zo daya cewar, su ya kamata su zabawa kansu shugaba ba wani daga waje ba.

Sai dai jam'iyyar PDPn a na ta bangaren tace, a matsayinta na uwa ba laifi ba ne ta yiwa 'ya'yanta jagora.

Masu lura da harkokin majalisa a Najeriyar dai na ganin ya kamata a kyale yan majalisar su zabi shugabannin da su ke ganin zasu iya jagorantar majalisar domin karfafa mulkin demokradiyya.