An wuce da shugaban asusun bada lamuni wani gidan yari

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dominique Strauss Kahn

Gidan yari dake can karshen gari Newyork shine wurin da ake ajiye rikakkun mambobin kungiyoyi masu aikata miyagun laifuka da aka yanke masu hukunci me tsauri.

Shugaban asusun bada Lamuni na duniya Dominique Strauss Kahn zai shafe kwana na uku a gidan yari bayan da alkalin wata kotu a Newyork ya hana bada belinsa bisa zargin yunkurin yi ma wata ma'aikaciyyar otel fyade.

Sai dai jami'ar hulda da jama'a na asusun bada lamuni Caroline Arkison ta ce hukumar zata cigaba da gudanar da kasuwancinta ba tare da wani tsaiko ba.

Hakazlika shugaban kungiyar ministocin kudi na taraya turai wanda shine firaministan Luxembourg Jean Claude Juncker ya nuna bakincikinsa game da lamarin.

Shugaban asusun IMF din dai zai kasance shi ka dai a cikin kurkukun kuma masu gadin gidan yari zasu rika sa ido akansa a sa'oi 24 ta kowace rana domin tabatar da tsaron lafiyarsa.