Za a bada belin matar Hosni Mubarak

Suzanne Mubarak
Image caption Ana zargin Suzanne Mubarak da mijinta da ya'yanta da cin hanci

A Masar, jami'ai sun ce babban mai gabatar da kara na kasar, ya bada umurnin a bada belin uwargidan tsohon shugaban kasar da aka kawar Hosni Mubarak.

A makon da ya wuce ne aka kama Suzanne Mubarak, yayin da ake ci gaba da bincike a kan batun cin hanci da rashawa a Masar din.

Jiya, kafofin yada labaran kasar sun bada rahoton cewa, Suzanne Mubarak ta yi alkawarin mika wa hukumomi wani gida a birnin Alkahira, da kuma dala miliyan ukku da ke ajiye a bankuna.

Tsohon shugaba Hosni Mubarak, da uwargidan tasa, da kuma 'ya'yansu biyu, dukansu suna tsere, yayin da ake zarginsu da tara haramtacciyar dukiya a tsawon mulkin shugaba Mubarak na shekaru talatin.

To sai dai sun musanta dukan zargin.