Kungiyar masu gasa biredi na yajin aiki a Niajeriya

Biredi
Image caption Jamaa na amfani sosai da biredi a Najeriya

A Najeriya a yau ne kungiyar masu gasa biredi da dangoginsa suka fara yajin aikin gamagari abisa dalilan da suka ce na tsadar garin fulawa da sauran kayan aikin gasa biredin.

Kungiyar ta yanke daukar wannan matakin ne a wani babban taron da ta gudanar a garin Shagamu na jahar Ogun ranar talatar da ta gabata, inda tace masu gidajen burodin a duk fadin kasar su dakatar da gasa biredin da dangoginsa daga yau, da kuma kawo karshen sayar da ragowar da suke da shi ya zuwa safiyar gobe laraba.

Kungiyar kuma ta ce za ta gudanar da zanga zangar lumana zuwa Fadar gwamnatoci da Majalisun jihohin kasar ranar Alhamis, domin bayyana damuwar su.